Thursday 5 February 2026 - 17:11
Waliyul Faqih, a matsayin Mataimakin Imam Mahdi (Ajtfs), na da alhakin Shiriyar da Al'umma da Kuma Gudanar da Dokokin Allah

Hauza/ Hazrat Ayatullah Nouri Hamedani ya bayyana cewa: "Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya samo asali ne daga imani na addini da kuma tushen Mahdawiyya, kuma ta hanyar samar da mahangar Wilayatul Faqih, ana daukarsa a matsayin mafi muhimmancin shimfida hanya don shirye-shiryen bayyanar Hazrat Waliyalul-Asr (Ajtfs) a lokacin Gaiba.

A wani rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza daga Hormozgan, Hazrat Ayatullah Nouri Hamedani, a cikin wani sakonsa ga taron kasa karo na biyar kan "Mahdawiyya da Juyin Juya Halin Musulunci," ya jaddada muhimmancin tushen tunanin Mahdawiyya a Musulunci da kuma Shi'a, inda ya bayyana cewa: "Mahdawiyya a koyaushe ta kasance wani dalili na wayar da kan al'ummar bil'adama, ayyukan yaki da zalunci, da kuma tawaye ga danniya a duk tsawon tarihi, kuma manufarsa ta karshe ita ce cikakken shiri na al'ummar bil'adama don karbar mulkin adalci na duniya.

Cikakken Sakon Hazrat Ayatullah Nouri Hamedani kamar haka yake:

DA SUNAN ALLAH, MAI RAHMA, MAI JINƘAI.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ubangijin Talikai, tsira da Aminci su tabbata ga shugabanmu kuma Annabinmu, Abu al-Qasim al-Mustafa Muhammad, da kuma danginsa tsarkaka masu tsabta, musamman ma wakilin Allah a Doron Kasa, kuma Allah Ya la'anci makiyansu gaba daya har zuwa ranar Sakamako.

Tare da sallama da gaisuwa ga watan jama'a mai girma da kuma ruhaniya, da kuma taya murna ga ranar haihuwar Ma'abocin Zamani, Wanda Al'ummai ke Jira, Hazrat Baqiyatullahil A'azam (Allah ya gaggauta bayyanarsa).

A cikin al'adar Shi'a, lokacin Gaiba, ana daukarsa a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci da tasiri, kuma Mahdawiyya a matsayin daya daga cikin muhimman dalilai a ayyukan yaki da zalunci da kuma tawaye ga danniya a tarihi, wanda manufarsa ita ce wayar da kan al'ummar bil'adama, kafa adalci, da kuma cikakken shiri na kowane mutum don karbar mulkin duniya, kuma babu shakka cewa wannan tunanin zai haifar da kafa zaman lafiya da tsaro da kuma nasara gaba daya ga bangaren gaskiya.

"Kuma Lalle ne Mun rubuta a cikin Zabur, bayan Ambatonmu (Alkur'ani), cewa hakika salihan bayina zasu gaji duniya." (Alkur'ani 21:105). Wannan aya tana nuni ne da cewa masu imani ya kamata su tsara rayuwarsu bisa ga wannan, kuma idan muka dauki Mahdawiyya a matsayin daya daga cikin mafi muhimman koyarwa na Shi'a kuma muka ba shi muhimmiyar rawa a cikin ayyukanmu na daidaiku da na al'umma, to, mun taimaka wajen cika taken Alkur'ani na mallakar duniya ga muminai, kuma wannan batu yana da matukar muhimmanci a gare mu cewa a cikin tunanin siyasa na Shi'a, Mahdawiyya wani ginshiki ne, kuma Juyin Juya Halin Musulunci wanda ya faru a zamaninmu kuma ya cika burin dukkan Imamai (AS) da malaman fikihu, an gina shi ne bisa ga Mahdawiyya.

A cikin juyin juya halin da suka faru a duniya, wasu dalilai ne ake kula da su, kamar halin zamantakewa, ko tattalin arziki, ko al'adu, ko siyasar waccan al'umma, kuma galibi shugabannin wadannan gwagwarmaya ba su kula da kiran na musamman ba bisa ga imani da addini ba. Amma juyin juya halinmu na Musulunci ya cimma nasara ne daidai da sabanin haka, wato, juyin juya hali ne na jama'a bisa ga imani na addini, wanda shi ne tushen Mahdawiyya. A wata ma'ana, tushe da kuma jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne Mahdawiyya, wanda a karshe zai kai ga bayyanar Imam Mahdi.

Ya kamata a lura cewa wannan juyin juya hali shi ne aiwatar da wannan tunanin siyasa, wato Mahdawiyya da Juyin Juya Halin Musulunci. Kuma mafi muhimmanci kuma mafi bayyanar wannan batu, wanda a ganina ya kasance wani tushe, shi ne cikakken aiwatar da ka'idar Jagorancin Waliyul Faqih a matsayin taimakon gaba daya malaman fikihu a fagen siyasa. Ya kamata a bayyana hakan ta yadda malamin fikihu mai cikakken sharudda, a matsayinsa na mataimakin Imamin Zamaninmu (Ajtfs), yana da alhakin jagorantar al'umma da kuma gudanar da dokokin Allah. Kuma wannan batu ba wai kawai a wani yanki na kasar ba ne, amma ga dukkan Musulmi a duk fadin duniya. Kuma bisa ga wannan ne muke da yakinin cewa Waliyul Faqih ba wai kawai a matsayin shugaban siyasa ba ne, amma yana wakiltar hasken wa'azin addini.

A bisa wannan, Imam Khumaini (Allah ya yi masa rahama) sau da yawa ya bayyana cewa wannan juyin juya halin da kuma tsarin Musulunci su ne shirye-shirye don bayyanar Imam Mahdi, kuma ya yi imani cewa dole ne koyaushe mu ci gaba da shirye-shiryen bayyanar sa. Kuma a cikin ruwayoyi akwai abubuwa makamantansu, wanda idan kana kwance a kan gadonka, to ya kasance akwai wuka a karkashin katifa kuma ka kasance a shirye don bayyanar sa, inda babu shakka wuka na nuni da shirye-shirye ne. Juyin Juya Halin Musulunci za a iya danganta shi da makomar gaba da kuma bayyanar Imam Mahdi. Yana da muhimmanci da kuma tilas mu raya a cikin ranmu dabi'ar rayuwa a zamanin bayyanar sa. Kuma wannan ba zai yiwu ba sai idan tsarin ilimi da iyali sun yi ƙoƙari sosai. Idan tsarin ilimi ba shi da matsayin al'ummar Mahdawa (Masu jiran Imam Mahdi) ba kuma iyalan ba su samar da hanyar rayuwar masu jira (Intizar ) ba, tabbas karkacewa za ta faru. A bisa wannan, kasancewar muna a wani zamani da muka kafa wata gwamnatin addini cikin falalar ubangiji, ya zama dole mu san darajar wannan gwamnati da kuma tsarin ci gaba na Wilayatul Faƙih, sannan kuma mu yi amfani da wannan babbar dama ta musamman domin bayyanar macecin al'ummar duniya.

Ya zama wajibi manyan mutane masana, musamman daga Hauza da Jami'o'i cikin nutsuwa su fuskanci barazanoni da suka bayyana a yau a sararin sadarwa, hankali na wucin gadi (AI), da irin wadannan batutuwa, musamman a bangaren ilimi da iyali, kuma su yi amfani da fa'idodin wadannan sabbin kayan aiki don hana hadari da cutarwa.

Kuma dukkan mu ya kamata mu sani cewa wannan juyin juya halin, wanda shi ne sakamakon jinin dubunnan shahidai da kuma matukar wahalar da al'ummar Iran da kuma jagorancin Imam mai girma ya haifar, za ta ci gaba da samun nasara ta hanyar jagorancin hikimar Jagora Mafi Girma, Ayatullah Khamenei, (Allah ya kare shi) har ta kai ga bayyanar Imam Mahdi. Insha Allah.

A karshe, ina rokon kasancewa cikin sojojin da ke hidima a karkashin Imamin Zamaninmu, Imam Sahib al-Zaman (AS) haka kuma wajibi ne in gode wa dukkan masu shirya taron Mahdawiyya da Juyin Juya Halin Musulunci, musamman Gidauniyar Addini ta Hazrat Mahdi Mau'oud (Ajtfs).

Kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya ba ku dukkanin nasara.

Hussein Nouri Hamedani

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha